1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin tsaftace wurare a kasar Mozambik

Sp. Loveday/Abdulraheem/BSApril 27, 2016

Amfani da dandalin sada zumunta na Facebook, wajen shawo kan al'umma shiga ayyukan tsaftace bola a fadin kasar Mozambik

https://p.dw.com/p/1IdWA
Videostill Mozambik Afrika Umweltverschmutzung
Hoto: DW

Bola da shara da duk wani irin nau'in datti, su ne abu na farko da baki ke tozali da su a Maputo babban birnin kasar Mozambik da ma titin gaabar tekun Miramar. To sai dai Carlos Serra Junior na cikin gamayyar masu rajin kawo sauyi 26 da suka sadaukar da lokacin su don kauda irin tarin bola da ke sauya fasalin biranen kasar. Carlos Serra Junior, ya ce sunyi amfani da kafar sada zumunta ta Facebook wajen hada kan al'umma, inda a yanzu suka gudanar da ayyukan tsaftace muhalli a cikin larduna hudu.

"A farko da muka sanar a facebook cewa zamu yi aikin shara ba wanda ya kula. To amma da muka yi a wurare 15, daga nan mutane suka soma karatun ta nitsu wajen zubda shara ko datti a ko ina."

Kilomita 15 daga bakin tekun Miramar a lokacin baya akwai itatuwan lambu na alfarma da ke a matsayin wuraren shakatawa, to amma a yanzu duk juji ya lullube su. Wannan ya sa wata 'yar fafutuka mai suna Liopoldina Gouveia ke nuna takaicinta kan haka.

"Abin takaici ne, a yanzu ba zan iya cin kifi ba, saboda dattin da muke watsawa shi ne kifin ke ci, don haka banga dalilin da zai sa inci kifin da muke watsa masu duk abin da ya zama datti a agaremu kuma mu sake ci a matsayin abinci ba."

A yanzu dai Carlors serra Junior na da burin sauya tunanin al'ummar Mozambik akan yadda za su rinka yi da datti ko bola, musamman don cin moriyar yanayi mai nagarta. Yayin da rana ke shirin fitowa, a kasar Mozambik rukunin matasa ne ke shan hantsi a akan yashin da ke bakin tekun Miramar. To sai dai, babban kalubale da ke gaban masu rajin tsabtace muhallin shi ne, yadda masu shakatawar ke barin kwalaben lemu a warwatse har wasu ke nutse wa cikin yashi.