Ta'addanci
Tsaro lokacin yakin neman zabe
November 3, 2022Talla
Sanarwar da ofisohin jakadancin Amirka da Birtaniya da Italiya suka fitar kan yiwuwar kai hare-haren ta’adanci a Abuja babban birnin Najeriya ta haifar da martani da zaman zullumi duk da matakan tsaro da ake kara dauka. Sai dai hukumin tsaro a Najeriya sun yi watsi da gargadin kai hare-hare a babban birnin tarayya Abuja da wasu manyan kasashen yammacin duniya suka yi. Hasali ma dai, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kara tsaurara tsaro a fadin kasar daidai lokacin da Amirka ta umurci ma'aikatan jakadancinta da zamansu bai zama dole a kasar ba su fice daga Abuja bisa yiwuwar kai hare-hare.