Tshisekedi na fuskantar jarrabawarsa ta farko
February 6, 2019Shugaba Felix Tshisekedi na fuskantar jarrabawarsa ta farko a matsayin shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sai dai ba daga 'yan adawa ba, a'a daga ma'aikata da suka shiga yajin aiki.
Tun bayan zaben ranar 30 ga watan Disamba rikicin kwadago musamman a ma'aikatun gwamnati ya ta'azzara yayin da kungiyoyin ma'aikata suka sanya fatansu kan sabuwar gwamnati karkashin tsohon jagoran 'yan adawa.
Yanzu dai ma'aikatan sun bukaci gwamnatin Shugaba Tshisekedi ta biya su bashin albashin da suke bin gwamnati wasu na tsawon watanni 38, sannan ta magance matsalar fifita wasu ma'aikata a kan wasu.
Ma'aikatan sufuri da na talabijin da inshora da jami'an kwana-kwana a wannan Laraba sun ci gaba da yajin aiki a lokacin da Tshisekedi ke a kasar Kenya a wata ziyarar aiki ta farko kasar waje.