Tshon shugaban Koriya ta Kudu na bijire wa yunkurin kama shi
January 2, 2025Hambararren shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ya ki mika kai domin a kama shi a rana ta uku a jere, yana mai shan alwashin ci gaba da bijire wa hukumomin da ke neman yi masa tambayoyi kan yunkurinsa da ya yi na kafa dokar ta-baci ta soji a kasar. A cikin wata sanarwar da ya fitar a birnin Seoul, tsohon shugaban ya ce Koriya ta Kudu na cikin hadari saboda dakarun cikin gida da na waje na barazana ga 'yancinta da ayyukan gudanar da gwamnati.
Karin bayani: Rikicin siyasa ya rincabe a Koriya ta Kudu
Dama dai, lauyoyinsa sun shigar da kara kan sammacin kama Mista Yoon, inda suka ce bai dace ba kuma ba shi da inganci. Sai dai Hukumar OIC da ke gudanar da bincike kan yunkurin tsohon shugaban Koriya ta Kudu ta yi gargadin cewa duk wanda ya kawo tarnaki ga kokarin kamun zai iya fuskantar tuhuma daga kotu. Wannan dai shi ne karo na uku cikin shekaru 25 da hukumomin Koriya ta Kudu ke gaza kama manyan jami'an gwamnati da kotuna ke nema ruwa a jallo, saboda dimbin magoya bayansu na hana ‘yan sanda cafke wadanda ake zargin a cikin kwanaki bakwai da doka ta kayyade.