1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Trump ya ce babu sassauci a akidarsa ta siyasar Amirka

June 27, 2021

Tsohon Shugaban Amirka Donald Trump ya sake nanata fushinsa da zaben da ya fitar da shi daga ofis, ya kuma ci gaba da ikirarin samun nasara duk dai ya kasa gabatar da hujjoji.

https://p.dw.com/p/3vcyZ
USA I Ex-Präsident Donald Trump startet neuen Wahlkampf
Hoto: Gaelen Morse/REUTERS

Kazalika ya lashi takobin daukar fansa ga duk wanda ya taimaka wurin tunbuke shi da majalisar kasar ta yi bayan da ya sauka daga mulki.  A ranar Asabar ne dai Trump ya hau munbari a wani gangami na siyasa a Jihar Ohio  a karon farko tun bayan saukarsa daga mulki, inda ya yi jawabi yana mai cewa

''Ba za mu taba hakura ba, ba kuma ba za mu taba komawa gefe guda ba. A siyasarmu babu alamar yin saranda. Ya ku 'yan uwana Amurkawa, har yanzu akidarmu tana nan ba ta canza ba. Abubuwan da suka wakana a baya somin tabi ne kawai.'


Trump dai ya samu sukunin yin wannan jawabi ne a gangamin siyasar da aka shirya don neman jam'iyyar Republican ta tsayar da dan takarar majalisar wakilan Amirka daga Jihar Ohia, inda Max Miller tsohon hadimin Trump a Fadar White ke neman kwace takarar jam'iyyar Republican din daga hannun dan majalisa mai ci wato Anthony Gonzalez wanda ke cikin 'yan majalisu 10 na Republican da suka goyi bayan tsige Shugaba Trump bayan da aka zargi tsohon shugaban na Amirka da ingiza 'yan daba su kawo rudani a cikin ginin majalisar kasar na Capitol a lokacin da ake hatsaniyar zaben kasar da ya gabata.