Sudan Tsohon Firaiministan ya rasu
November 26, 2020Marigayi al-Mahdi shi ne zababben Firaiminista na karshe a kasar Sudan sama da shekaru 20, bayan da tsohon Shugaban kasar Omal al-Bashir ya kawar da shi a shekarar 1989. Sadik al-Mahdi ya rasu yana shekaru 84.
Ya kasance babban mai adawa da tsohuwar gwamnatin Sudan da aka yi wa juyin mulki. A shekarar 2018 ne al-Mahdi ya koma Sudan bayan dogon lokaci yana gudun hijira a birnin Alkahira na kasar Masar, ya bar Sudan bayan takun saka tsakaninsa da gwamnatin al-Bashir ya yi zafi kan yadda yake samun karbuwa sakamakon jagorantar muryoyin al'umma domin nuna fushinsu kan matsin tattalin arziki a Sudan.
'Yarsa Mariam mataimakiyar jam'iyyar Umma Party, na cikin wadanda aka tsare bayan gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin tsohon Shugaba al-Bashir.