SiyasaAsiya
Tsohon Firaministan Indiya Manmohan Singh ya rasu
December 26, 2024Talla
Tsohon FiraministanIndiya Manmohan Singh ya rasu a ranar Alhamis a birnin New Delhi bayan fama da rashin lafiya.
Singh ya yi wa'adin farko da kuma na biyu a lokacin jagorancinsa sannan ya habaka tattalin arzikin Indiya a lokacin da ya ke ministan kudi.
Mutum 46 sun mutu a bikin wankan tsarki na addinin Hindu
Tsohon Firaministan ya rasu ya na da shekara 92 a duniya kuma ya yi farin jini a kasar a lokacin mulkinsa.
Da farko masanin tattalin arziki ne kafun ya rikide ya zama dan siyasa da kuma gwamnan babban bankin kasar.
Indiya da Chaina za su yi sulhu kan iyakar da ke tsakaninsu
Kafafen yada labaran Indiya sun ruwaito cewa an garzaya asibiti da shi a birnin Dew Delhi bayan ya fara rashin lafiya kafun rai ya yi halinsa.