Tsohon madugun yakin Laberiya ya rasu
November 28, 2024Talla
An ba da labarin mutuwar tsohon madugun yakin Laberiya, Prince Johnson, mutumin da ya aikata mumunar ta'asa lokacin yakin basasar kasar a tsakanin shekarun 1989 zuwa 2003.
Prince Johnson, wanda daga bisani ya taka rawa a siyasar Laberiya, inda ya zama dan majalisar dattawa; ya mutu ne a ranar Alhamis yana da shekaru 72.
A cikin shekara 1990 wani faifan bidiyo ya nuno Johnson na kurbar barasa lokacin da mayakansa ke azaftar da marigayi Shugaba Samuel Doe har ya sheka lahira.
Kisan na tsohon shugaban Laberiya Samuel Doe ne dai ya zamo silar fadawar kasar cikin yakin basasar da ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane dubu 250, sannan kuma ya yi matukar ruguza tattalin arzikin kasar.