Tsohon shugaban Kenya Arap Moi ya mutu
February 4, 2020Talla
Tsohon shugaban kasar Kenya Daniel Arap Moi wanda ya yi mulkin na tsawon shekaru 24 ya mutu da safiyar wannan Talata (04.02.2020). Shugaba mai ci a yanzu Uhuru Kenyatta ne ya yi wannan sanarwa, inda ya bayar da umarnin zaman makomi na kasa baki daya har sai an yi jana'izar tsohon shugaban ba tare da tantance rana ba.
Daniel Arap Moi wanda malamin makaranta ne ya gaji wanda ya samar wa Kenya da ‘yancin kanta wato Jomo Kenyatta lokacin da ya mutu shekaru 42 da suka gabata. Sai dai ya gudanar da salon mulkin kama karya inda ya yi ta daure abokan hamayya tare da azabtar da jama'a. Sannan kuma cin hanci ya zama ruwan dare a Kenya zamanin Arap moi yayin da rashin aikin yi ya yi katutu.