Tsohon shugaban Kenya Mwai Kibaki ya rasu
April 22, 2022Talla
Tsohon shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ne ya sanar da rasuwar.
'Yace tare da jimami muna sanar da sanar da komawar shugaba Kibaki ga mahallicinsa, ya bauta wa kasarsa da kishi da nagarta wanda za a iya dangantawa tun zamanin gwagwarmayar kwatar yanci".
Tshohon shugaban ya bauta wa Kenya da Afrika da kuma duniya baki daya. Mutum ne na iyali kuma abokin kowa.