1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugunne ba ta kare ba a Sudan ta Kudu

April 22, 2014

'Yan tawaye sun karyata zargin cewa sun aikata kisan kiyashi, amma kuma ana cigaba da samun rahotannin kissan fararen hula babu gaira ba dalili

https://p.dw.com/p/1BmLL
Rebellen ethnische Massaker in Südsudan
Hoto: AFP/Getty Images

Yan tawayen dake goyon bayan tsofon mataimakin Shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Macher, sun musanta zargin da Majalisar Dinkin Duniya take musu na cewar sun aikata kisan kiyashi a kan mutane fiye da 200 a garin Bintiu da ke da arzikin man fetur.

Yan tawayen dai sun yi zargin cewa wadanda suka aikata kisan, tsakanin sojojin da gwamnati ta yi haya domin su yake su ne da wadanda tsautsayi ya fada masu yayin dauki ba dadin da ya afku tsakanin dakarun gwamnati da na yan tawaye. Kamar yadda Kakakin Shugaban yan tawayne James Gatddet Dak ya bayyana:

"Wannan ba gaskiya bane, mayakan mu bas u kashe fararen hula ba. Abin da ya faru shi ne an yi batakashi tsakanin mu da sojojin gwamnati, Waɗannan su ne daga cikin wadanda suka samu raunin da muka samu, saboda haka mayakan da suka shiga cikin fadar mu da gwamnati ne. domin mu bamu kai hari kan wani farin hula ba. Idan kuma akwai wadanda suka rasa rayukan su daga cikinsu to sai dai a dalilin batakashin da ya wakana a lokacin, saboda a irin wannan lokacin ba wanda ke sanin harsashin da ya yi ajalin wani."

Rebellen ethnische Massaker in Südsudan
Kissa bisa dalilai na kabilanciHoto: Reuters

Wasu na zargi da hannun Omar al-Bashir na Sudan

A halin yanzu gwamnatin Sudan ta Kudu na zargin Sudan ta arewa da ke karkashin mulkin Shugaba Omar Hassan al-Bashir, da goyawa yan tawaye baya wajen amfani da 'yan tawayen Janjaweed domin yin yaki a yankin Bentiu

Kimanin Sojojin Majalisar Dinkin Duniya dake aikin wanzar da zaman lafiya 8,000 ne suka bazu a yankin da ke fama da wannan tashin hankalin. Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu Joseph Contreras ya ce ko a wannan Talatar Sojojin Majalisar Dinkin Duniya sunyi ga gawarwakin sojoji da fararen hula

"Sojojin sun ga kimanin gawawwaki 35 zuwa 40 a gefen hanya, mafi yawancin matatun kuma suna sanye ne da inifom din sojoji yayinda kadan daga ciki suka kasance fararen hula, kana a wani gurin kuma dubban fararen hula ne wadanda suka rasa matsugunnensu suka yi dandazo, musaman a asibitin Bentui da kuma harabar hukumar samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya.

Barazanar Yunwa

Majalisar ta kuma yi gargadin cewa sama da mutane miliyan guda na fiskantar hadarin fadawa cikin bala'in yunwa, tare da wasu miliyan biyar da ke bukatar agaji kana kimanin fararen Hula 80,000 ne suka fake a cikin sansanin sojojin Majalisar Dikin Duniya domin gudun kada a kawo musu farmaki.

Kasar uganda na tallafawa bangaran Shugaba Salva Kiir da jiragen yaki, a yayin da su kuma bangaren yan tawaye su ke samun goyon baya daga mayakan sa kai da aka fi sani da white army.

Südsudan UN-Camp in Bor
Sansanin MDD a BorHoto: AFP/Getty Images

Wuraran da tashin hankalin yafi shafa sun hada da arewa da arewa maso gabashin yankunan jihohin Unity, Upper Nile da kuma jihar Jonglei.

A yazu haka dai manazarta na ganin cewa kasar Sudan ta Kudu wacce ta kasance jaririyar kasa a duniya ta kama hanyar rugujewa bayan makonni hudun da aka shafe ana yakin basasa a cikinta wanda ya hada da kisan kiyashi bisa dalilai na kabilanci, al-amarin da ya kai ga lalata akasarin kudaden tallafin da gwamnatin kasar ta samu bayan da ta samu yancin kanta.

Mawallafiya: Zainab Babbaji Katagum
Edita: Pinado Abdu Waba