1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin 'yan jarida da laifin cin amanar kasa a Turkiyya

Yusuf BalaMarch 25, 2016

Can Dundar, babban edita a gidan jaridar Cumhuriyet, da Erdem Gul na ofishin jaridar da ke birnin Ankara ana zarginsu da kitsa makarkashiya ga kasa.

https://p.dw.com/p/1IK2l
Symbolbild Erdem Gul
Erdem Gul da Can Dundar a taron manema labaraiHoto: picture-alliance/dpa/D. Photos

Wata kotu a kasar Turkiyya ta dauki matakin sauraron karar wasu fitattun 'yan jarida a bayan idanun al'umma da ma daukar shugaban kasar Tayyip Recep Erdogan a matsayin wanda ya gabatar da karar sun aikata ba daidai ba, lamarin da ke ci gaba da samun suka ta al'ummomin kasa da kasa.

Can Dundar, babban edita a gidan jaridar Cumhuriyet, da Erdem Gul na ofishin jaridar da ke birnin Ankara ana zarginsu da kitsa makarkashiya ta ganin an kifar da gwamnatin wannan kasa ta Turkiya, zargin da ya biyo bayan bada wani hoton bidiyo a watan Mayu wanda ya nuna hoton jami'an leken asiri na kasar, na kokari na tallafa wa wata mota makamare da makamai da za ta je Siriya a shekarar 2014. Erdem Gul dai ya ce matakin da kotun ta dauka ba zai sa su karaya ba.

"Wannan matsaya ce da kotun tsarin mulki ta dauka kuma abu ne da ke a zahiri abu ne da ta saba, muna fiskantar tuhuma da za ta iya kaimu ga karasa rayuwarmu gidan kaso dan muna aikinmu amma ba zamu karaya ba."