Tura ta kai bango tsakanin Amirka da Falasdinu
December 9, 2017Talla
A cewar Majdi al-Khaldi babban mai bai wa Abbas shawara kan harkokin diflomasiya, babu wata ganawa da za ta auku tsakanin mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence da kuma shugaban Falasdinu Mahmud Abbas. Inda ya kara da cewa Amirka ta kai koluluwar karya yarjejeniya, bayan da ta yanke shawar maido da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.
A wani abun da ya shafi rikicin wutar da Trump ya kunna a tsakanin Yahudawa da Larabawa, a kalla mutane hudu suka mutu a birnin Gaza, bayan da Isra'ila ta kai farmaki da jiragen yaki.