Turkiyya: Samar da shugaba mai cikakken iko
January 9, 2017Talla
Baya ga batu na baiwa shugaba iko cikakke kamar yadda ake da su a wasu kasashen duniya, yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Turkiyya din zai bada dama ga Shugaba Racep Tayyib Erdogan hurumin iya ci gaba da kasancewa kan shugabancin kasar har ya zuwa shekara ta 2029. Idan dai har majalisar dokokin ta amince da gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar, to kuwa wannan zai kasance karo na farko da kasar ta Turkiyya ta kaddamar da tsarin mulkin Shugaba mai cikakken iko. Majalisar dokokin za ta share kimanin makwanni biyu ta na tafka muhawara kan matakin kafin ta bayyana matsayinta a kai.