1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda a Beljiyam sun gano tutar 'yan Is

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 16, 2016

'Yan sanda a kasar Beljiyam sun sanar da cewa sun gano tutar kungiyar 'yan ta'addan IS cikin gidan da suka kai wani samame a Brussels babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1IEEq
'Yan sanda na farautar 'yan ta'adda a Beljiyam
'Yan sanda na farautar 'yan ta'adda a BeljiyamHoto: Reuters/Y. Herman

Samamen na birnin Brussels dai 'yan sandan sun kai shi ne a ci gaba da binciken maharan birnin Paris na kasar Faransa da mahukuntan Beljiyam din ke yi. Haka kuma jami'an tsaron kasar sun sanar da cewa mutum guda da ya mutu yayin musayar wuta a lokacin binciken na ranar Talata 15 ga wannan wata na Maris da muke ciki, dan asalin kasar Aljeriya ne da yake zaune a kasar ba bisa ka'ida ba. A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar kakakin mai gabatar da kara na gwamnatin kasar ta Beljiyam Eric Van der Spyt ya yi karin haske yana mai cewa:

"Guda daga cikin maharan da ya mutu yayin wannan arangama sakamakon yunkurin bude wuta ga jami'an 'yan sanda, an gano cewa dan asalin kasar Aljeriya ne mai suna Belkaid Mohammed da aka haifeshi a ranar tara ga watan Yuli na shekatra ta 1980. Yana zaune ne ba bisa ka'ida ba kana 'yan sanda basu taba kama shi da wani laifi ba in ban da sau guda a shekara ta 2014 sakamakon laifin sata."

Kawo yanzu ana ci gaba da neman mutane biyu ruwa a jallo, da suma suka tsere daga wannan gidan bayan samamen 'yan sandan.