An zargi Chaina da rikicin Hong-Kong
August 20, 2019A cikin wani sako da ya wallafa a ranar Litinin, kamfanin Twitter ya ce bayan bankado matsalar ya dakatar da aikin wasu shafukan Twitter 936 wadanda a bisa goyon bayan gwamnatin Chaina ke aiki tare wajen yin farfagandar kawo goyon baya ga gwamnatin Hong-Kong, baya ga wasu da dama shafukan na Twitter sama da dubu 200 na kasar ta Chaina da ya dakatar da aikinsu.
Shi ma dai daga nashi bangare kamfanin Facebook ya sanar da shafe bayanan da ke cikin wasu shafukan sadarwar na Facebook na wasu mutanen da ke da alaka da gwamnatin ta Bejin, baya ga wasu shafukan sama da dubu 15 da ya shafe a baya.
Sai dai kamfanonin biyu ba su bayyana tasirin da matakin nasu ya yi ba wajen rage kaifin farfagandar da Chainar ke yi wajen rarraba kawunan masu zanga-zangar neman sauyin na Hong-Kong.