Ukraine na neman karin tallafin daga kawayenta
February 17, 2024Talla
A jawabinsa a taron tsaron shekara-shekara kan tsaro na birnin Munich da ke Jamus karo na 60, Zalensky ya ce idan har ba a dauki matakin gaggawa ba, shugaba Putin na Rasha zai samu nasarar haddasa bala'i a cikin shekaru masu zuwa.
Kalaman na Shugaba Zelensky na Ukraine na zuwa ne bayan da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi kira ga kasashen Turai da su yi koyi da gwamnatin Berlin na bayar da karin tallafin yaki ga Ukraine. Gwamnatin Jamus ta amince da bai wa Ukraine karin tallafin makamai yayin da Kyiv ke shiga shekaru uku na yaki da Rasha.