Ukraine ta ce ba za ta bari Kirimiya ta kubuce mata ba
March 8, 2014Ministan harkokin wajen Ukraine din na rikon kwarya ya ambata hakan a wannan Asabar din, inda ya kara da cewar yankin na karkashin Ukraine kuma zai cigaba da kasancewar karkashin kulawarta sannan gwamnatinsu ba za ta bari wajen ya fada hannun kowacce kasa ba.
A wani labarin kuma, gwamnatin Rasha ta ce za ta hana dukannin wani aiki da ake yi na sanya idanu kan makamanta muddin aka cigaba da yi mata baraza saboda matsayin da ta dauka kan yankin Kirimiya wanda suke takaddama kansa da kasar Ukraine.
Fadar mulki ta Kremlin dai ta ce ta dau wannan mataki ne saboda barazanar da ake cigaba da yi mata da ma zarge-zargen da ta ke fuskanta daga yammacin duniya wandanda ta ce ba su da tushe bare makama.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman