Kira domin sasantawa da 'yan IS
March 13, 2015Asusun na UNICEF dai ya ce ya yi wannan kira ne domin samun damar kai agaji ga kanana yaran da ke yankunan da suke karkashin IS din. A cewar daya daga cikin mambobin asusun Hanaa Singer dole ne a dauki wannan mataki domin a ceto rayuwar dinbin kananan yaran da ke cinkin garari. Ta shaidawa manema labarai a birnin Geneva cewa sun dade suna bibiyar 'yan IS din domin su basu dama amma sun ki su yi magana da su, tana mai cewa bawai alhakin kungiyoyin bada agaji bane kadai tallafawa wadanda ke cikin taskun ya zama wajibi sauran sassan da ke cikin rikicin su sanya baki. Suma sauran kungiyoyin bada agaji na Majalisar ta Dinkin Duniya sun bayyana cewa suna son kai agaji ga miliyoyin fararen hula da ke cikin halin tasku a yankunan da ke karkashin ikon IS din, sai dai kungiyar ta ki saurarar su.