1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Ta ce akwai tamowa ga yaran Rohingya

Abdourahamane Hassane
December 22, 2017

Asusun yara kanana na MDD UNICEF ya ce kishi daya bisa hudu na yara kanana 'yan kasa da shekaru biyar 'yan kabilar Rohingya na Bama wadanda suka yi hijira zuwa Bangladesh na fama da matsalar karancin abinci.

https://p.dw.com/p/2ppst
Bangladesch | Humanitäre Hilfe für Rohingya
Hoto: DW/ P. Vishwanathan

Kakakin kungiyar ta  UNICEF Christophe Boulierac ya ce a wasu jerin bincike da aka gudanar har' sau uku daga cikin watan Oktoba zuwa Disamba da ya gabata. Ya nuna cewar har zuwa kishi 25 cikin dari na yaran 'yan kasa da shekaru biyar na fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.