UNICEF ta damu da kashe yara a Kabul
August 16, 2018Talla
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana takaici kan yadda yara ke ci gaba da rasa rayukansu, a rikice-rikicen da ke faruwa a Afghanistan.
UNICEF din na magana ne bayan wani hari mai muni da aka kai kan wata cibiyar ilimi na 'yan Shi'a a ranar Laraba, inda aka halaka kananan yara 67 wadanda ke rubuta jarrabawa a Kabul, babban birnin kasar.
Majalisar ta Dinkin Duniya ta kuma yi kiran mutunta hakkin jama'a, musamman kare kananan yara, ganin rashin dacewarsu da hare-hare na ta'adda.
Tuni ma dai Shugaba Ashraf Ghani na Kasar ta Afghanistan, ya yi Allah wadai da harin na jiya Laraba, ya kuma sanya a gudanar da cikakken bincike.