1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara sama da 3000 aka tilasta wa shiga aikin soja

April 12, 2019

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ko UNICEF ya ce yara ‘yan kasa da shekaru 18 guda 3,500 kungiyoyin na masu gwagwarmaya da makamai su ka tilasta wa shiga yaki tun daga shekara ta 2013 zuwa yanzu.

https://p.dw.com/p/3GhGD
Südsudan - Kindersoldaten
Hoto: Getty Images/AFP/C. Lomodong

Tun can baya Kungiyouin kare hakin bani adama ke baiyana damuwa kan yadda mayaka ke amfani da yara 'yan shekaru tsakanin goma zuwa sha bakwai shiga harkokin yaki, abin da su ka ce ya sabawa yarjeniyoyin kasa da kasa mai kare hakkin yara. A wani rahoto da ofishin kula da yara na majalisar dinkin duniya ya fitar,  ya nuna cewa akwai yiwuwar wadannan alkaluma ya zarta 3,500 saboda akwai wasu yaran da har yanzu ba a iya kai wa garesu domin sanin yawan su ba.

Nigeria Maiduguri Flüchtlingslager
UNICEF ya baiyana kaduwa kan sakamakon rahoton banaHoto: Reuters/A. Akinleye

Haka rahoton ya bayyana cewa akwai wasu yara kimanin 432 da aka kashe ko dai a hare-hare ko kuma yayin da ake gallaza musu azaba da kuma wasu yara 180 da ake zargin mayakan sun sace su tare da cin zarafin mata da ‘yan mata akalla arba'in da uku a shekarar da ta gabata. Malam Ibrahim Yusuf daya daga cikin shugabannin kungiyoyin fararen hula ne a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya a cewar sa, wadannan alkaluma ba su kai yawan yaran da kungiyoyin masu gwagwarmaya ke amfani da su a fagen yaki ba. Kungiyoyi na masu gwaagwarmaya kamar  Boko Haram ba su taba boye amfani da yara wajen yaki ba inda ake iya gani a wasu fayafayen bidiyo ko hotuna da kungiyar ta sha wallafa.

Amfanin da yara wajen yaki a cewar majalisar dinkin duniya abin tashin hankali ne kuma ya zama dole a tashi tsaye domin a bai wa yara damar yin rayuwa mai inganci tare da ba su ilimin da ya dace don su ne manyan gobe. Dangane da yadda ake zargin kungiyoyin gwagwarmayar da cin zarafin mata kuma Kungiyoyin kare hakkin mata da yara sun ce ba kan su matsalar ta tsaya ba don ta shafi cin zarafin mata a wannan sashe na Najeriya.