UNICEF: Yaran Libiya na cikin hadari
September 24, 2018Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce rayuwar yara kanana kimanin dubu 500 ce ke cikin hadari a birnin Tripoli a sakamakon kazaman fadan da ke gudana tsakanin bangarori dabam-dabam a kusa da birnin yau kusan wata daya da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 115 wasu 400 suka jikkata.
Hukumar ta UNICEF ta ce a jumulce kananan yara miliyad biyu da dubu dari shida ne ke bukatar taimako a fadin kasar ta Libiya inda fadace-fadacen baya bayan nan suka tilasta wa iyalai dubu daya da 200 barin gidajensu inda yanzu adadin 'yan gudun hijirar acikin kasar ya kai sama da mutun dubu 25.
Kazalika ta ce baya ga matsalar ruwan sha da ta abinci da makamashi, yaran kasar ta Libiya na fuskantar yaduwar cutar kyanda a tsakaninsu inda yanzu haka ta kama yara sama da 500.
A kan haka ne ma ministan harakokin wajen kasar Faransa Jean Yves Ledrian ya yi kira da a dauki mataki kan mutanen da ke kawo cikas ga shirin tsagaita wuta da na zaman lafiya a kasar ta Libiya.