UNITA a Angola za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓe
September 2, 2012Talla
Wani kakkakin jam'iyyar ya ce suna da takardun na shaidu, da suka tattara daga rufunan zaɓe inda suke da wakilai ,wanda ke nuna cewar sakamakon da hukumar ta baiyana ba shi ba ne ke cikin hannun wakilan su.
Sakamakon wuccin gadi da hukumar ta baiyana na nuna cewar jam'iyyar yan addawar ta UNITA na da kishi 17 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa. Yayin da jam'iyyar da ke yin mulkin ta MPLA ta sami kishi 74, abin da ke baiwa shugaba José Eduardo Dos Santo damar yin wani sabon wa'adin na mulki.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe