1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Valerie Amos ta fara wata ziyara a Sudan ta Kudu

January 27, 2014

Shugabar hukumar kula da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos, ta fara ziyara a Sudan ta kudu wadda ke daf da fadawa cikin wata babbar matsalar harkokin agaji.

https://p.dw.com/p/1Axtz
Valerie Amos Südsudan
Hoto: AP

Wannan ziyara ta Valerie Amos, ta tsawon kwanaki uku, tana yin tane a cewar Majalisar Dinkin Duniya domin janyo hankulan kasashen duniya kan wannan kasa, dake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati dake biyayya ga shugaba Salva Kiir, da na 'yan tawaye masu biyayya ga Riek Machar.

Masu fada da juna a wannan jaririyar kasa, na ta zargin junansu da ci gaba da kai hari duk da jarjejeniyar tsagaita wutar da aka sa ma hannu a ranar Alhamis (23.01.14) da ta gabata.

Kawo yanzu dai rikicin ya haddasa mutuwar dubunnan mutane tun daga tsakiyar watan Disamba da ya gabata, yayin da wasu mutane fiye da 700,000. ke gudun hijira.

A cewar wakilin Asusun kula da lafiyar kanana Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef, annobar cutar kyanda da ta barke a wani sansanin 'yan gudun hijirar da ya cika makil da jama'a,tayi sanadiyar mutuwar a kalla yara 30.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Saleh Umar Saleh