1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce rundunar soji na da zabi na yin biyayya

Ramatu Garba Baba
February 19, 2019

Shugaban Amirka Donald Trump ya nemi rundunar sojin kasar Venezuela kan ta amince da Juan Guaido a matsayin shugaban kasa ko kuma ta yi biyu babu a rikicin da ake kan madafun iko.

https://p.dw.com/p/3DcrU
Venezuela Militär
Hoto: Getty Images/AFP/F. Parra

A yayin da ake ci gaba da fafutuka kan mulkin kasar Venezuela, ne Shugaba Trump ya gana da wasu 'yan asalin kasar a Amirkan, ya fada musu cewa kada su manta idanun duniya na kan Venezuela, kuma ya dace rundunar sojan ta karbi tayin da madugun adawa ya musu, don mara masa baya a kokarinsa na karbe ragamar mulki daga hannun Nicolas Maduro, Trump ya ce alfanun yin hakan, na da yawan gaske, don sojojin da iyalansu za su tsira daga duk wata tuhuma su kuma ci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali akasin hakan zai janyo musu asarar da ba za ta misaltu ba inji Trump, wato muddun suka bari aka karbe mulki daga Maduro.

Juan Guaido ya ja daga, inda ya tsayar da ranar ashirin da uku na wannan watan na Febrairu, a matsayin ranar da za a gudanar da aikin gama gari na shigo da kayayyakin agaji da gwamnati mai ci ta harmata a shigo mata dasu, ana ganin samun nasarar shigo da agajin ga mabukata da ke cikin tsanani na karancin abinci da magunguna zai taka rawa ainun a cimma muradunsa na zama shugaban kasa.