Wakilai a taron Bali sun bukaci zage dantse wajen kare muhalli
December 8, 2007Wata kwarya kwaryar yarjejeniya da aka gabatar a taron dumamar yanayi dake gudana a tsibirin Balin kasar Indonesia,tayi kira ga kasashen duniya dasu mike tsaye wajen kalubalantar kowane irin bala’i da ka iya aukuwa sakamakon sauyin yanayi.Yarjejeniyar wadda wakilan kasashen Indonesia da Australia da Afrika ta kudu,suka rubuta ,na nuni dacewa kokarin da akeyi yanzu na rage hayakin masana’antu,ba zai isa yin wani tasiri ba.Taron wanda ke samun halartan wakilan kasashe 190,nada nufin samo hanyoyin da zaa cimma sabuwar yarjejeniya wadda zata maye gurbin na Kyoto ,wadda wa’adinta ke karewa a 2012.Cibiyar tattauna harkokin muhalli ta Majalisar Dunkin Duniya dai ,ta sanar dacewa ana kann hanyar cimma sabuwar yarjejeniya.Sai dai tuni Amurka ta nunar da adawarta dangane bukatun kasashen duniya na ta amince da rage hayaki mai guba da masana’antun ta ke fitarwa.