Wakilan manyan kasashe sun bijire wa taron Saudiyya
October 18, 2018Manyan ministocin kasashen Birtaniya da Faransa da na Holland, sun sanar da janyewarsu daga halartar babban taron nan kan harkokin saka jari da za a yi a Saudiyya a makon gobe, saboda damuwa kan bacewar dan jaridar nan dan Saudiyya, Jamal Khashoggi.
Shi ma sakataren baitul malin Amirka, Steven Mnuchin, ya bayyana janyewarsa daga halartar taron, dai dai kuma lokacin da Shugaba Donald Trump ke kaffa-kaffa da batun, saboda kawancen Amirka da Saudiyya.
Amirkar dai kamar Birtaniya da kuma Faransa, manyan kasashe ne da ke sayar da makamansu ga Saudiyya.
A halin da ake ciki ma dai Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo, ya shaida wa Shugaba Trump cewa akwai bukatar bai wa Saudiyyar lokaci don ta kammala bincikenta kan batun na Khashoggi,
Mr. Pompeo, ya ziyarci Saudiyya da ma Turkiyya dangane da batun.