1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilan MDD, sun isa Sudan ta Kudu

August 12, 2014

Wakilan kashe 15 membobi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun soma wata ziyara ta kwanaki biyu daga wannan Talata (12.08.2014) a Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1Ct2s
Hoto: DW/G. Tedla HG

Kasar ta Sudan ta Kudu dai, ta shiga halin kaka nikayi bayan da aka shafe watanni 8 ana gwabza fada, sannan ga barazanar fadawa cikin mungun kangi na yunwa da dubunnan 'yan gudun hijirar suke ciki. Dubunnan mutane ne dai suka hallaka, sakamakon wannan fada,sannan kuma wasu mutanen a kalla milian daya da dubu dari biyar sun bar matsugunnan su. Wa'adin da aka bayar dai na kwanaki 60 domin bengarorin biyu na shugaban kasar Salva Kiir, da na madugun 'yan tawayan Riek Mashar su kafa gwamnatin hadin kan 'yan kasa ya kawo karshe tun a ranar Lahadi ba tare da sun cimma daidaito ba. Masu ziyarar na kwamitin sulhun na MDD zasu tataunawa da brengarorin kasar, tare da ganewa idanun su halin da al'ummar kasar ke ciki.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu