Mata na samun karin sukuni a Saudiyya
September 2, 2019Talla
Mahukuntan na Saudiyya dai sun amince da wasu sabin dokoki ne da ke bai wa matan karin 'yanci, ciki har'da ba su damar yin fasfo da yin bulaguro su kadai ba tare da muharraminsu ba. Haka kuma sabuwar dokar ta bai wa matan damar sanar da auransu da kuma damar karbar takardar sakinsu kai tsaye daga kotu, ba sai ta hannun mahaifi ko maharraminsu ba.