Wani jirgi mai saukar Ungulu ya faɗi a Iraƙi
August 12, 2014Talla
Daga cikin waɗanda suka jikkata, har da 'yar Majalisar dokokin nan, ta ƙabilar Yazidis ƙabilar tsirarun ƙasar, da wani ɗan jarida na jaridar New York Times ta ƙasar Amirka da ke cikin jirgin wanda shi ma ya samu rauni.
Jirgin mai saukar ungulu ya faɗi ne bayan tashinsa a yankin nan na Sinjar, yayin da yake ɗauke da 'yan gudun hijira da kuma kayayyakin agaji, sai dai har yanzu ba'a gano dalilan faɗuwar jirgin ba.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane