Wani jirgin ƙasa na ƙasar Indiya ya yi hatsari a gabacin ƙasar
May 28, 2010Wani abu da ya fashe a gabacin ƙasar Indiya, ya yi sanadiyar kaucewar wani jirgin ƙasa daga kan hanyarsa. Jirgin wanda ya taso daga Bombai zuwa Cal-culta ya kuma ci karo da wani jirgin ƙasar da ke ɗauke da kayayakin yan kasuwa.
Mutane a ƙalla guda 65 suka mutu a sakamakon wannan hatsari da ake kyautata zaton cewa ƙungiyar yan tawayye na Maoiste sune umul-haba'isin aukuwar haɗarin.
Gidan Talabijin na ƙasar ya nuno hotunan tarkacen jirgin da ya yi kaca kaca, wanda kuma wasu da dama daga cikin fasinjojin suke sarƙe cikin tarkacen ,
Ministan sufurin jiragen ƙasa na Indiya Mamata Banerjee, wanda ya tabbatar da cewa yan tawaye sune suka ɗana bam ɗin, ya shedda cewa a kwai yiwuwar samun ƙaruwar adadin mutane da hatsarin ya rutsa da su.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane.
Edita : Abdullahi Tanko Bala.