Wariya ga nakasassu a duniya
May 30, 2013A ranar wannan Alhamis (30.05.13) ce Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton da ke cewar, kananan yara wadanda ke fama da nakasa ne aka fi nunawa wariya da kuma yin watsi da su wajen gudanar da al'amuran duniya. Rahoton ya kara da cewar, sau da dama hatta rajistar haihuwa ma ba a yi musu, kuma ana zaluncesu yayin hulda, a wani lokacin ma harda kissansu.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Dniya UNICEF, wanda ya fitar da rahoton game da halin da kananan yara ke ciki a duniya na shekara ta 2013, ya ce galibin matsalolin da kananan yara da ke fama da nakasa ke fuskanta, ba sa fitowa fili.
Darektan asusun Anthony Lake ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP, gabannin fitar da rahoton a birnin Vienna na kasar Austria cewar, yara da ke fama da nakasa sun fi hadarin ci gaba da zama cikin talauci, da rashin samun ilimi da kuma kula da lafiyarsu. Rahoton ya bayar da misali da irin wariyar da kananan yara zabaya ke fama da ita a kasar Tanzaniya, inda a wasu lokutan ake kashesu.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar