Wata ta ci zarafin shugaba Mugabe
November 3, 2017Talla
'Yan sandan kasar Zimbabuwe, sun kama wata 'yar kasar Amirka da ke a kasar, saboda zarginta da cin mutuncin shugaban kasar Robert Mugabe. Ita dai matar, Martha O'Donovan, ana zarginta ne da kiran shugaba Mugabe mai son zuciya da rashin sanin ya kamata, kalaman da ta watsa a shafinta na Twitter.
Wannan dai shi ne kame na farko da aka yi a kasar bayan kafa ma'aikatar tsaron harkokin sadarwar Intanet a watan jiya. 'Yan sandan dai sun kama ta bayan kai samame gidan inda suka cika hannu da wayarta ta hannu da ma sauran na'urorin Komfuta. Sai dai matar ta musanta zargin da ake yi mata.