Wata tirela ta salwantar da mutane a Kenya
July 1, 2023Talla
Lamarin wanda ya faru da yammacin Juma'a, ya afka da mutane ne da ke a wani yanki da aka kira Londiani da ke yammacin kasar ta Kenya. Akwai ma wasu gommman mutanen da suka ji munanan raunuka a lamarin na kasar Kenya.
Shugaba William Ruta na Kenya, ya bayyana alhininsa da ta al'umar kasar ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin.
Ma'aikatar kula da harkokin sufuri ta ce wannan lamarin ya sanya su fara shirye-shiryen kawar da kasuwar da ke kimanin mil 200 arewa maso yammacin Nairobi babban birnin kasar.
Tirelar da ta isa wajen a guje dai ta murkushe motoci da babura da dama da ke a gefen hanyar da ta afka wa da yammacin na jiya.