1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Watan azumi ya shigo cikin kalubalen tsaro

Larwana Malam Hami/PAWJune 18, 2015

A yayin da aka shiga wata mai tsarki na Ramadana mai falala, an cigaba da ganin hare-hare, inda tun a jajibirin azumin aka kai wasu hare-haren yankin Diffa.

https://p.dw.com/p/1FjJX
Nigeria Ramadan Fastenbrechen in Sokoto
Hoto: DW/A. Abdullahi

A Jamhuriyar Nijar musulmi sun bi sahun takwarorinsu na wasu kasashen duniya wajen fara azumin watan Ramadana bayan da majalisar musulunci ta kasa ta tabattar da tsayuwar jinjirin watan a yankuna da dama na kasar.

Sai dai farashin kayan marmari irin na buda baki da suka hada da dangin 'ya'yan itatuwa ya karu a kasuwanni daga jihohin Diffa da ke fama da rikicin Boko Haram da kuma jihar Damagaram, lamarin da tuni ya sa malaman da ke gabatar da wa'azi suka fara nasiha tare da bayana irin falalar da watan azumin ke tattare da ita bayan aikata aikin lada komin kankantar sa.

Rahotannin hare-hare a wasu yankunan Diffa
Tun daga ranar farko ta azumin Ramadana a sassan gabashin kasar daga Damagaram zuwa Diffa talakawa sun fara korafi da wasu daga cikin farashin kayan bude baki kamar dankalin turawa zuwa mangoro da ma su salati, inda a Diffa mai fama da rikicin Boko Haram talakawan ke korafi da tsadar rayuwar.

Amadu dan Kori na kungiyar yaki da tsadar rayuwa a cewar sa a zagayen da suka yi a ranar farko ta azumin farashin ya hau kuma ya mika sako ga al'umma. To sai dai rohotanni daga jahar ta Diffa na cewar a daren jiya wayewar yau wasu mutane da ake zargin yan boko Haram ne sun kai hari wasu garuruwan kauyen na Diffa, inda suka karkashe mutane da dama.

Flüchtlingsfamilie aus Nigeria bei Diffa Niger
'Yan gudun hijira na Zaman zullumi a DiffaHoto: DW/Larwana Malam Hami

To amma a lokacin da na tuntubi gwamnan jahar ta Diffa Yakubu Sumna Gao ya ce yana kan hanya ta zuwa garin amman idan ya dawo zai tuntubeni don y kara mani haske.