1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Wayar da kai bisa cutar daji

Abdul-raheem Hassan SB)(MAB
May 11, 2022

Hope Wambui na kan bakarta na kawo sauyi a babbar unguwar marasa galihu ta Kenya mai suna Kibera, matashiyar na fadakarwa kan batutuwa kan cutar daji da kayayyakin tsaftar mata, ta hanyar wasan kwaikwayo.

https://p.dw.com/p/4B83u
GKI-Projekt | Crisis Communication Chapters
Hoto: Wiliam Oloo/DW

Hope Wambui mai kimanin shekaru 10 a duniya, na cikin taurari mafi haskawa a unguwar marasa galihi da ake kira Kibera a wajen Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Matashiyar ba ta jin kunyar gabatar da manyan batutuwa. Unguwar Kibera, yanki ne mai fama da talauci kuma iyalai da yawa suna kokawa don samun abinci.

Kashi 65 cikin 100, na mata da 'yan matan Kenya, ba za su iya biyan kuɗin kwalliya ba. Ba sabon abu ba ne a Kibera wasu 'yan mata na daukar matakan da suka dace don kawai su ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullun, kamar yadda Regina WAithera, mahaifiyar Hope ke cewa.

Ganin irin kalubale da yara mata ke fuskanta, matashiya Hope na da sabbin dabarun taimakawa.

Hope da mahaifiyarta, suna ba da audugar mata kyauta ga waɗanda ke buƙata, shirin, mai suna "Hope Beyond Hope" yana samun tallafi ne ta hanyar gudummawa daga masu fatan alheri da kuma tallace-tallace daga kayan kwalliyar Hope. Suna kuma ba da azuzuwan tsaftar lokaci tare da koya wa 'yan matan sabbin dabaru don saita su kan hanyar samun 'yancin kai na kuɗi.