Weah zai kwaskware kundin tsarin mulkin Laberiya
January 30, 2018Kundin tsarin mulkin ya tanadi haramta wa wadanda ba bakar fata ba takardar iznin zaman dan kasa a kasar ta Laberiya.
Shugaba Weah ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban 'yan majalissun kasar a jiya Litinin inda kuma ya soki lamirin matakin da ke haramta wa 'yan asalin kasashen waje mallakar filin noma, matakin da ya ce na taimakawa ga hana masu niyyar saka jari na ketare zuwa cikin kasar.
Kazalika shugaban na Laberiya ya soki lamrin matakin da ke haramta wa 'yan kasar ta laberiya izinin mallakar takardar izinin zaman dan kasa a wata kasar ta daban, matakin da ya ce bai dace ba ta la'akari da yadda 'yan aksar ta laberiya da dama da suka bar kasar a loakcin yakin basasa na shekarun 1989 zuwa 2003 sun fake a wasu kasashen inda aka kuma ba su takardar izinin zaman 'yan kasa.
Bugu da kari Shugaba Weah ya sanar da cewa zai rage kudin albashi da na wasu alawus nasa da kashi 25 daga cikin dari kana ya yi kira ga 'yan majalissun kasar suma su yi haka.