WHO: Akwai hadari zuwa Angola
April 26, 2016Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana a ranar Talatan nan cewa duk mutumin da ke son tafiya zuwa kasar Angola ya zame masa wajibi ya tabbatar na dauke da katin na shedar yin allurar rigakafin cutar shawara ko yellow fever a Turance.
Hukumar ta WHO ta bayyana cewa akwai fargaba sosai ta yiwuwar kamuwa da wannan cuta ta shawara a sassa daban-daban na biranen kasar ciki kuwa har da birnin Luanda da ke zama babban birnin kasar.
Wannan cuta dai na ci gaba da yaduwa a wannan kasa ta Angola tun daga watan Disambar bara inda aka samu mutane 1,975 da suka harbu da kwayoyin wannan cuta yayin da 258 suka rasu ta sanadinta.
A cewar WHO ya zuwa yanzu mutane miliyan bakwai ne aka yi wa allurar rigakafi na wannan cuta ta shawara tun bayan da aka fara aikin rigakafi a watan Fabrairu na wannan shekara.