Tedros ya yi tazarce a shugabancin WHO
May 25, 2022Talla
Mai shekaru 57 a duniya dan asalin kasar Habasha, ya yi tazarce a matsayin darakta janar na hukumar ta WHO din ne bayan da aka zabe shi da gagarumin rinjaye kasancewar ba shi da abokin hamayya. Tun dai a shekara ta 2017 ne, Tedros ya dare kan kujerara shugabancin hukumar ta WHO a matsayin dan asalin Afirka na farko da ya taba samun wannan mukami. A wancan lokaci ya yi alkawarin samar da harkokin kiwon lafiya cikin sauki ga kowa a baki dayan duniya, sai dai a shekara ta 2020 annobar corona ta sha kan al'amura baki daya. Tuni dai Tedros ya amince da sake zaben nasa da aka yi, cikin yanayi na zubar da hawaye.