WHO ta ce za a iya kawar da corona a 2022
January 24, 2022Talla
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce akwai yiwuwar kawo karshen mummunan lokaci da duniya ke ciki na cutar corona a wannan shekarar, idan kasashe suka yi amfani da duk kayan aikin da ake da su.
"Yana da hatsari mu yi imanin cewa Omicron shi ne karshen nau'in cutar coorona, wannan yana nufin akwai yiwuwar sake barkewar sabbin nau'uka. Rayuwa da cutar ba ya nufin ba wa cutar damar hawan kawara, wannan baya nufin mun mika kai ga mutuwar kusan mutane 50,000 a mako daya. Allura kadai ba ita ce makamin yakin cutar ba, har sai mun cimma burinmu na ganin kowace kasa ta yi wa kaso 70 cikin 100 na al'ummarta rigakafin nan da tsakiyar 2022."