Kenya: Ruto ya yi kiran da a zauna lafiya
August 16, 2022Talla
Sabon shugaban Kenya yayi kira ga al'umma da su kwantar da hankula sa'annan ya sha alwashin yin aiki domin gina kasarsa "Ina so in yi wa al'ummar Kenya alkawarin cewar, zan gudanar da mulkin dimukaradiyya cikin haske da adalci, za mu yi aiki tare da 'yan adawa ta yada za su iya saka ido a kan yadda muke tafiyar da mulki. Kafin bayyana sakamakon zaben hudu daga cikin manbobi bakwai na hukumar zaben sun nisanta kansu daga sakamakon. An samu barkewar zanga-zanga a Kisumu da ke a yankin arewacin kasar ta Kenya da kuma yankunan da ke kusa da Nairobi babban birnin kasar jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben da magoyan bayan Raila Odinga suka yi zargin cewar an tafka magudi.