William Tubman:Wanda ya zamanartar da Laberiya
August 30, 2020Yaya aka raini William Tubman?
An haifi William Vacanarat Shadrach Tubman ranar 29 ga watan Nuwamba 1895. Ya fito daga yankin kudu maso gabashin Laberiya, daga garin da ake kira Harper na gundumar Maryland. Sunan wuraren ya yi kama da na Amirka, saboda Jamhuriyar Laberiya ta ayyana samun 'yanci daga Amirka a shekarar 1947 da 'yantattun bayi suka yi, wadanda suka dawo daga Amirka a lokuta dabam-dabam a tsawon shekaru 50 a farkon karnin. Mahaifin Tubman yana cikin 'yantattun bayi 69 da suka tafi Laberiya a shekarar 1944. Mahaifiyarsa ta fito daga Atlanta, Georgia.
Tubman ya girma karkashin kulawar mahaifinsa mai wanda ya gwada wa 'ya'yansa tafarkin addini na yin addu'a da hana yaran kwanciya a kan gado saboda kar su shagala.
Da me William Tubman ya yi suna?
Tubman, wanda ya kasance shugaban Laberiya na 19, da kuma ya jagoranci kasar daga shekarar 1944 zuwa 1971, mutum ne da ake yi wa kirarin baban Laberiya na zamani. Ta hanyar amfani da dukiyar da masu saka jari suka samar a kasar, ya gina hanyoyin mota da na jiragen kasa tare ma da inganta matsayin tashar jiragen ruwa da ke Monrovia babban birnin kasar. Haka nan ya samar da ingantaccen yanayi na fitar da roba da tama da karafa zuwa kasashen duniya. Bayan mutuwar William Tubman, Laberiya tana da babbar cibiya ta kasuwanci da ta yi suna a duniya. Yawancin muhimman gine-gine irinsu majalisa da zauren taro na Monrovia da cibiyar daukaka al'adu da a yanzu ake kira Kendeja, duk sun samu ne a zamaninsa. Hakazalika, shi ne ya gina fitaccen katafaren Otel din nan wato Ducor International, daya daga cikin fitattun Otel a yammacin Afirka.
Ko William Tubman ya samar da rayuwa mai inganci da al'umar Laberiya?
Lokacin mulkin Tubman, Laberiya ta samu bunkasa. Gwamnatinsa ta kyautata fannonin ilimi da lafiya. Kasar ta rungumi tsarin yaki da jahilci da ake yi wa lakabi da "Each one teach one". Wani abin kuma shi ne, Tubman ya yi kokarin daidaita tare da hada kan 'yan Laberiya. 'Yan kasar da ke da karfin fada a ji masu alaka da Amirka sun muzguna wa 'yan kasar cikin wasu shekaru kusan shekaru 100. Sai dai gwamnatin Tubman ta tabbatar da tsarin bai daya na 'yanci tsakanin mutane.
Amma, mulkin shekaru 27 na William Tubman bai rasa samun suka daga wasu bangarori na kasar ba. Yakin basasar da ya auku a shekarun 1980, abu ne da ya sanya alakanta shi da samo asali daga ginshikin da tsohon shugaban ya kafa. An dai zarge shi da kama-karya da kuma rayuwa ta bushasha. Haka nan alakarsa ta kut-da-kut da Amirka ta sanya wasu cewa ita ta raba kasar da 'yancinta. Domin girmama shi da abubuwan da ya samar, an ware ranar haihuwarsa a matsayin ranar hutu a fadin kasar.
Wasu kalamai fitattu da William Tubman ya yi a baya?
"Laberiya ba ta samu diyyar mulkin mallaka ba"
"Ba mu kaddamar da yaki kan tsarin gurguzu ba, muddin dai bai wuce iyaka ba, amma muna iya yakar duk wani yunkuri na tilasta mu yin abin da ya wuce hankalinmu".
Wannan makala ta sami tallafi daga masana tarihi irin su Farfesa Doulaye Konaté da Lily Mafela, Ph.D. da kuma farfesa Christopher Ogbogbo.
Gidauniyar Gerda Henkel ce ta dauki nauyin wannan shiri na Tushen Afirka.