250512 Israel Flüchtlinge Afrika
May 30, 2012Dubbannin 'yan gudun hijira daga ƙasashen Afirka daban daban da suka haɗa da Sudan da Eritriya ne ke yin tururuwa zuwa Isra'ila domin neman mafaka a 'yan shekarun baya bayannan, saɓanin yanda lamarin yake a da, ko da shike kuma yawan su bai taka kara ya karya ba - idan an kwatanta da 'yan gudun hijirar Afirka dake kwarara zuwa yankin Gabas Ta Tsakiya. Sai dai kuma hukumomin Isra'ila sunƙi amincewa da basu takardun izinin zama 'yan ƙasa, inda a maimakon haka suke ɗaukar su a matsayin masu neman mafaka domin gudun kar su gurgunta manufar kasancewar Isra'ila ƙasar Yahudawa ne kaɗai, abinda kuma ya saɓawa yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya akan mutumin daya dace ya zama ɗan gudun hijira.
Lardin Hatikva dake kudancin birnin Tel Aviv na ƙasar ta Isra'ila, yanki ne dake ƙunshe da dubbannin 'yan gudun hijira da kuma masu neman mafaka daga Afirkar, inda kuma aka samu wasu 'yan Isra'ilar dake nuna adawar su da masu neman mafakar, harma da gudanar da wata zanga- zangar da ta ƙunshi Miri Regev, 'yan majalisar dokokin Isra'ila daga jam'iyyar Likud, wadda ta kwatanta masu neman mafaka daga Sudan a matsayin annoba ga tsarin rayuwar Yahudawa.
'Yan gudun hijira kimanin dubu 60 da ake tafka muhawara akansu a Isra'ila sun tsallako zuwa Ira'ila ne ta yankin Sina'i dake ƙasar Masar, galibinsu kuma tare da taimakon masu fasakwaurin jama'a.
Ministan kula da harkokin cikin gidan Isra'ila Eli Yischai wanda ke cikin masu zanga zangarya ce galibin 'yan gudun hijirar da suka zo Isra'ila ba saboda dalilan jin ƙai bane, amma na tattalin arziƙi ne. Akan hakane ya bayyana buƙatar korar su:
" Ya ce babu wata ƙasa a duniyar nan dake mutunta bil'adama kamar Isra'ila. Kusan kowace shari'ar da ta shafi korar baƙi, kotun ƙoli ta janyo mata cikas. Babu wata ƙasa a duniyar nan da za ta rungumi irin wannan ɗabi'ar. Idan har zan sami dama, to, kuwa cikin tsukin shekara guda babu wani ɗan gudun hiujirar da zai saura anan Isra'ila. Da taimakon Allah za mu ci gaba da kare matsayin kasancewar Isra'ila ta Yahudawa mai burin cimma kare muradunsu."
Masu adawa da kuma masu son 'yan gudun hijira a Isra'ila
Yischai ya ƙara da cewar akwai da dama daga cikin Yahudawan dake tunani irin nasa, domin kuwa a ganin su alkwai 'yan gudun hijira musamman daga ƙasashen Afirkar dake da hannu cikin yiwa mata fyaɗe da fashi da makami, abinda yasa suke kallon su a matsayin masu aikata manyan laifuka.
Sai dai kuma hukumomin ƙasar sun zargin masu boren da neman ingiza fitina, wanda kuma wata ƙungiyar dake fafutukar zaman lafiya ta nemi babban mai shari'a na ƙasar daya binciki gaskiyar hakan.
A dai Isra'ilar, akwai wasu 'yan ƙasar dake ɗora fushin su akan gwamnati da kuma hukumomin dake kula da yankunan su maimakon 'yan gudun hijira daga Afirka, suna masu zargin hukumomin da rashin yin katabus wajen inganta rayuwar su.
Wannan Matar cewa take gwamnati ba ta taimaka mata da komi ba duk da cewar tana zama a kudancin Tel Aviv tun a shekara ta 1976 ba tare da kyakyawar rayuwar ba.
Shi kuwa wannan bayahuden tsokaci yake game babakeren wasu mutane wajen mallakar filaye da yin manyan gine ginen ƙasaita. "
Shugaban 'yan Sanda Yohannan Danino a birnin Tel Aviv ya bada shawarar baiwa 'yan gudun hijirar takardun izinin yin aiki a ƙarƙashin doka a matsayin hanyar kawo ƙarshen aikata laifuka.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh/Teichmann,Torsten
Edita : Yahouza Sadissou