Wunin karshe na tsagaita wuta a Gaza
August 7, 2014Yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki ukun da ke aiki a Zirin Gaza, wadda ta kawo sassauci sosai ga milliyoyin mutane a yankin, ta shiga wuni na karshe. Isra'ila dai ta nuna cewa a shirye ta ke ta kara wa'adin, amma kuma kungiyar Hamas tana jan kafa wajen amincewa da hakan, bisa la'akari da wasu bukatunta da take hankoron ganin an cimma.
Wata majiyar diplomasiyya ta fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa, kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus a na su waje, sun shirya wani tayi sun gabatarwa Isra'ila da Falasdinu da Masar da mahukuntan Washington, wanda suke gani idan har aka aiwatar, zai biya mahimman bukatun da bangarorin biyu suke son ganin an cimma kafin su bada kai.
Wata majiyar gwamnatin Israila ta ce Israila a shirye ta ke ta tsagaita wuta baki daya, kuma ministan kudin kasar Yair lapid ya tabbatar da hakan, lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai:
"Muna matakin tattaunawa ta diplomasiyya ne, kuma wajibi ne a mayar da hankali kan sake gyara, da kwance dammara. Tilas ne kasashen duniya su matsawa Hamas lamba, ta mika rokokinta, domin a samu a sake gina Zirin Gaza ta yadda za ta sami zaman lafiya da kwanciyar hankali".
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu