SiyasaArewacin Amurka
Wuta kusa da ginin majalisar Amirka
January 18, 2021Talla
An rufe zauren majalisar dokokin Amirka na wani lokaci sakamakon hayaki da aka gani daga wani gini da ke nesa da wurin, lokacin da ake aikin kwaji kan rantsar da sabon Shugaba Joe Biden.
Hukumomin tsaron Amirka sun ce babu wata barazana ga rayuwar mutane kuma sun yi imani babu barazana lokacin da za a rantsar da Joe Biden a jibi Laraba.
Tuni Shugaba mai barin gado Donald Trump ya ce ba zai halarcin bikin rantsuwar ba, abin da aka dade ba a gani ba a tsarin Amirka, amma mataimakin shugaban kasa mai garin gado Mike Pence zai halarci bikin rantsuwar tare da sauran tsaffin shugabannin Amirka.