Wutar rikici na ci gaba da ci a Sudan
February 4, 2019Talla
'Yan sanda a Sudan na ci gaba da amfani da karfi kan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Omar al Bashir, inda suka yi masu ruwan barkonon tsohuwa a manyan biranen Karthoum da kuma Umdurman.
Daruruwan masu zanga zanga sun mamaye manyan biranen a wannan Litinin, inda suka yi ta nuna Allah wadai da tsarin da kasar ke ciki, suna mai kiran samun 'yanci da kwanciyar hankali.
Shugaban kasar da wasu masu fada a ji, na cewa ne duk wani ikirarin sauyi, tilas ne ya kasance ta hanyar zabe ba kuma ta zanga-zangar ba.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce kimanin mutane 51 suka salwanta sakamakon boren, yayin da hukumomin Sudan din ke cewa mutane 30 ne suka mutu.