1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

080808 Angola Wahlkampf

Cascais, António (DW Portugiesisch)August 8, 2008

An ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe a ƙasar Angola.

https://p.dw.com/p/Et9N
Tutar Angola



Hukumar zaɓe a ƙasar Angola ta busa ƙafan yaƙin neman zaɓen ´yan Majalisun dokoki da za a shirya ranar 5 ga watan Satumber.

Angola ta samun ´yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Portugal a shekara ta 1975.

Tun daga wannan lokaci wannan shine karo na biyu da ´yan ƙasar za su zaɓen yan Majalisar dokoki.

Sunyi zaɓen farko yau da shekaru 16 da su ka gabata, to saidai bayan wannan zaɓe, ƙasar ta faɗa cikin wani saban yaƙin bassasa, a sakamakonmatakin da shugaban Ƙungiyar tawayen UNITA Jonas Savimbi ya ɗauka na zargi gwamnati da tafka maguɗi.

A shekara ta 2002, bayan mutuwar Savimbi, UNITA da jam´iyar MPLA mai riƙe da ragar mulki suka ratatta hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya  a ƙasar Angola, bayan yaƙin bassasa da ya hadasa mutuwar mutane kimanin rabin miliyan.

Zaben na ranar 5 ga watan Satumbaer na matsayin zakaran gwajin dafi da shgugaba Eduardo Dos santos da ke rike da ragamar mulkin ƙasar Angola tun shekaru 30 da suka wuce.

Fernado Tati na ɗaya daga ƙusoshin jam´iyar MPLA ya kuma bayyana cewar jam´iyar za ta samu gagaramin rinjaye:

"Muna gudanar da aiki ne ta yadda za mu lashe wannan zaɓe tare da babban rinjaye, wanda zai bamu damar mulkin ƙasar ba tare da munyi haɗin gwiwa ba, gwamnatin haɗin gwiwa na maida ƙasa baya."

A halin da ake ciki dai, yaƙin neman zaɓe ya kankama, ako ina cikin titina, ´yan takara sun liƙa hotuna, tare da tutocin jam´iyunsu.

To saidai jam´iyar UNITA ta zargi MPLA da yin amfani da dukiyar ƙasa wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe , kazalika, ta na zargin jam´iya mai rike da ragamar mulki ,da shirya maguɗi, Alberto da Costa Junior shine kakakin jam´iyar UNITA.

"ɗauki misali ayar kudin zaɓe mai lamba 134 wadda ta tanadi cewar idan wata runfar zaɓe ta yi rijistan masu zaɓe 250, amma a wajen ƙidayar ƙuri´a domin tantance yawan wanda suka yi zaɓe, idan aka samu ƙuri´a 500 da su za a aiki, shin ina adalci a nan wurin ?"

Adalci ko zalunci, a  jimilce dai, mutane kimanin miliyan takwas ne za su zaɓi ´yan majalisar dokoki 220,wanda suka fito daga jam´iyun siyasa  guda goma.

Tunni, masu sa ido  daga Ƙungiyar Tarayya Turai, da Ƙungiyar Tarayya Afrika sun fara isa a ƙasar Angola,domin shaidar yadda yaƙin neman zaɓen zai wakana.