Yadda ake watsi da 'yancin yara a wurare da ake tashin hankali
A ranar 20 ga watan Nuwamban ko wace shekara ce ake bikin yara ta duniya. Tun a shekarar 1989 Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar don tabbatar da 'yancin yara. Amma har yanzu ana take hakkin yaran a wasu wurare.
Yara da ke tasowa a cikin baraguzan gine-gine
Yara na cikin hadari musamman a wurare da ake fama da yaki kamar Gaza. Suna iya rasa muhallansu ko su ji rauni ko a kashe su ko kuma a shigar da su aikin soja. Yara na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a harin Hamas kan Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktoban 2023. Alkaluman Falasdinawa sun nuna yara sama da 11,000 ne suka rasu tun da aka fara yaki a Gaza.
Rashin tabbas kan makoma
Wannan yaron ya rasa kafarsa a yakin da ake yi a Sudan. Makasudin amincewa da 'yancin yara da Majalisar Dinkin Duniya ta yi shi ne kare yaran daga yake-yake. Amma shekara 35 bayan amincewa da 'yancin nasu lamarin bai inganta ba. A 2023 an samu karin kashi 21% na cin zarafin yara a wurare da ake fama da tashin hankali.
Yadda yaki ya lalata wani ajin karatun yara
Wannan wata makarantar yara ce da aka lalata a sansanin 'yan gudun hijira sakamakon yaki a Syria. Akalla dai yaron ya samu kujerar zama. Makarantu da yawa sun lalace gaba daya tun fara yakin a 2011,sannan an mayar da sauran kuma mafaka na gaggawa. Majalisar Dinkin Duniya ta fada cewa kusan rabin yara da rikici ya daidaita a duniya ba su iya zuwa makaranta.
Dukkan yara na da 'yanci iri daya a duk inda suke a duniya
A rubuce a cewar MDD dukkan yara suna da 'yanci iri daya ba tare da la'akari da inda suka fito ko jinsi ko addininsu ba. Wannan 'yancin kuwa ya hada da na kiwon lafiya da ilimi da ba su damarmaki da kuma karesu daga fitina su kuma yi wasa su ji dadi yadda ya kamata. To amma a zahiri lamarin ba haka yake ba. A New Delhi an tilasta wa wannan yaron tsince-tsdince a Bola cikin hayaki mai guba.
Yadda ake haifar yara cikin tashin hankali
Yara da ake haifa a wuraren da ake yaki na fuskantar tashin hankali da kuma rashin isashshen kiwon lafiya da ruwa mai tsafta da kuma abinci mai kyau kamar yadda kungiyar kare hakkin yara ta Save the Children ke cewa a yayin da yakin Ukraine ya cika kwanaki 1,000 da barkewa. An haifi yara sama da rabin miliyan daya tun lokacin da Rasha ta far wa Ukraine a Fabrairun 2022.
Sauyin yanayi na kara yi wa yara barazana
Sauyin yanayi da ke haddasa guguwa irin Man-yi, wacce ta far wa Philippines a kwanan baya da ta kasance ta shida a cikin wata guda na kara jefa iyalai cikin tasku musamman a kudancin duniya. A dalilin wannan yara na shan wahala sakamakon yunwa da rashin ilimi da kiwon lafiya da kuma rabuwa da iyayensu.
'Yara na bukatar kariya sosai daga wajenmu'
Ana fama da yunwa musamman a zirin Gaza inda aka ga wannan yarinyar rungume da guntun burodi a watan Yuni. Kusan kashi uku na al'ummar duniya 'yan kasa da shekara 18 ne kuma yara su ne suka fi fuskantar tashin hankali. "Akasari ana watsi da 'yancinsu," a cewar Boris Breyer, mai magana da yawun hukumar SOS da ke Jamus. "Yara na bukatar kariya sosai daga wajenmu." a cewar Breyer.
Yarinya tana leke a shingen da ke tsakanin Mexico da Amurka
'Yan cirani da yawa sun damu kan komawar Trump shugabancin Amurka a wa'adi na biyu. Trump ya yi barazanar korar 'yan cirani sosai baya ga raba da dama da yaransu a wa'adin mulkinsa na farko. Amurka ce kadai kasar da ba ta rattaba hannu kan 'yancin yara ba a duk cikin kasashen Majalisar Dinkin Duniya.
Rashin makoma mai kyau ga yara
Rashin makoma mai kyau ga yara matsala ce da ta fi ta'azzara a sansanonin gudun hijira a Myanmar. "Yaran Rohingya na girma babu fatan makoma mai kyau" a cewar Jasna Causevic ta kungiyar masu fusknatar barazana. "Yunwa da tashin hankali da nuna wariya sun dabaibaye rayuwar yaran kuma ba a cika maida hankali kan makomarsu ba" Sama da yara 500,000 na rayuwa a sansanoni irin wannan a Bangladesh.
Yara mata ba su zuwa makaranta
Alkaluman hukumar kula da ilimi da al'adu ta MDD UNESCO sun nuna yara mata miliyan 1.4 a Afghanistan aka hana zuwa makarantar sakandare "lamarin da ya jefa rayuwar mutane na karni guda cikin tasku," a cewar UNESCO. Yanayin samun abincinsu ma ya ragu matuka tun da Taliban ta karbi mulki shekaru uku da suka gabata: 10% na yara 'yan kasa da shekara biyar suna fama da rashin abinci mai gina jiki.
Ana tilasta wa yara aiki
Wannan yaron da ke fasa bulo da guduma a birnin Dhaka na Bangladesh, ya na daya daga cikin yara miliyan 160 a duniya da suke aiki a yanayi na hadari. Wannan lamarin na karuwa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a wani sabon bincikenta kan bautar da yara. Akasari talauci ne ke kawo hakan saboda ana tilasta wa yara su taimaka wa iyali.