1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amura na kara dagulewa a Sudan

April 20, 2023

Sudan ta sake fadawa cikin rikicin da ke kama da juyin mulki da ya rikide ya koma yaki a wannan mako duk da kokarin da ake yi na kashe wutar. Kimanin mutum 270 ne suka mutu.

https://p.dw.com/p/4QMgS
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance / AA

Bayan wata gajeruwar tsagaita wuta da aka samu a Sudan, wadda ta ba da damar janye mutanen da suka sami raunuka da kuma ficewa da fararen hular da rikicin ya ritsa da su, fadan ya sake ci gaba a birnin Khartoum da ma wasu jihohin kasar, a daidai lokacin da ake dakon shiga tsakanin na kasashe da sauran manyan kungiyoyi na duniya. Rikici ne dai tsakanain sojojin gwamnati da mayakan rundunar ko ta kwana ta RSF karkashin ikon Janar Mohammad Hamdan Dagalo. Tuni ma dai aka soma zargin cewa akwai manyan kasashen da hannunsu ke cikin wannan rikici wanda kawo i yanzu aka rasa rayukan akalla mutum 270. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka wakana a yakin da aka shiga rana ta shida da fara shi kuma cikin watan Ramadana.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna